Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana cewa za a zabi wani Kirista dan kudu a matsayin abokin takararsa a zaben 2023.
Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ya ruwaito cewa, an yi ta cece-kuce kan wadanda ‘yan takarar shugaban kasa za su zaba a matsayin abokin takararsu yayin da wa’adin ranar 17 ga watan Yuni da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta kayyade don gabatar da jerin sunayen ‘yan takarar ya gabato.
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya fito a kwanan baya kan wanda zai yanke shawarar zaba a matsayin mataimakinsa.
Da yake magana da jaridar The PUNCH, Kwankwaso ya ce, a halin yanzu jam’iyyar NNPP tana tuntubar juna, domin zabar kiristoci mai kishin kudancin kasar nan.