Babban kamfanin man fetur na kasa, NNPCL ya musanta raɗe-raɗin sayar da matatar mai ta birnin Fatakwal.
Shugaban kamfanin Bashiru Ojulari ne ya bayyana haka a wani taron tuntuɓa da kamfanin ya shirya a shalkwatarsa da ke Abuja.
Ojulari ya ce NNPCL ba shi da aniyar sayar da wata matata mallakinta, sai dai ma ƙoƙarin gyara su domin yin daidai da zamani.
An fara raɗe-raɗin sayar da matatar ne bayan wata hira da shugaban kamfanin ya yi a taron OPEC a birnin Vienna na ƙasar Austria a farkon watannan.
A lokacin Ojulari ya yi wata hira da jaridar Bloomberg, kan batun sayar da matatar inda ya ce “komai zai iya faruwa”.
Tun daga wancan lokacin ne aka yi ta maganganu game da makomar matatar.