Babban kamfanin mai na Najeriya, NNPCL, ya ce, ya kammala duk wasu shirye-shirye don fara ɗauko tataccen man fetur daga matatar mai ta Dangote domin shigar da shi kasuwannin ƙasar a yau Lahadi.
NNPCL ɗin ne dama ya sanya yau Lahadi, 15 ga watan Satumba a matsayin ranar da zai fara dakon man na Dangote.
Cikin wani saƙo da kamfanin ya wallafa a a shafinsa na X, ranar Asabar ya ce ya shirya manyan motocin dakon mai a harabar matatar da ke unguwar Ibeju-Lekki a birnin Legas, domin lodin man.
Ana sa ran shigar man Dangoten kasuwa, zai kawo sauƙi ga matsalar mai da ƙasar ke fuskanta a baya-bayan nan.
A baya-bayan nan ne dai NNPCL ya sanar da ƙarin kuɗin man fetur a ƙasar, lamarin da ‘yan ƙasar da dama ke kokawa a kansa