Kamfanin samar da man fetur na ƙasar NNPCL ya fara kai ɗanyen man fetur don ayyukan tace mai na gwaji a matatar man fetur ta Fatakwal.
Jaridar Punch ta dai ambato wasu jami’ai na NNPCL na tabbatar mata da hakan, kuma ta ƙara da cewa dillalan man fetur su ma sun shaida mata wannan al’amari, da kuma cewa matatar za ta riƙa tace man fetur da dizal da kuma sauran nau’o’in mai don jihohin Najeriya 12 ciki har da Abia da Rivers da Akwa Ibom da Delta.
Ta ce NNPPCL ya shaida mata cewa nan gaba kaɗan za a kammala ayyukan tace mai na gwaji da ake yi a matatar Fatakwal, don fara tace ɗanyen man fetur da za a iya sayarwa a kasuwa.
A ranar 21 ga watan Disamba ne, gwamnatin Najeriya ta ba da sanarwar cewa an kammala wasu gyare-gyare a wani sashe da ake kira Area-5 na matatar Fatakwal da ke cikin jihar Rivers.
Ta ce ɓangaren farko na matatar ya kammala kuma za ta fara tace ɗanyen man fetur ganga 60,000 a kullum bayan hutun Kirsimeti.
Rahoton na zuwa ne yayin da ƙungiyar ƙwadago ta NLC a ranar Lahadi ta soki lamirin gwamnati saboda abin da ta kira gazawarta wajen cika alƙawurra da yawa da ta yi wa ‘yan Najeriya ciki har da alƙawarin cewa matatar man fetur ta Fatakwal za ta fara aiki a wannan wata na Disamba.