fidelitybank

NNPCL ba su fara daukar man fetur din mu ba – Dangote

Date:

A ranar Alhamis ne kungiyar Dangote ta musanta rahotannin da ke cewa kamfanin man fetur na Najeriya, NPL, ya fara dauke mai daga matatarsa.

An bayyana cewa, NNPCL ya dauko man fetur daga matatar Dangote ya sayar wa ‘yan Najeriya kan Naira 897 kan kowace lita.

Rahoton ya zo ne a daidai lokacin da Shugaban Rukunin Dangote, Aliko Dangote ya bayyana cewa matatar man a shirye take ta fara hakowa da kuma sayar da albarkatun man fetur.

Sai dai Anthony Chiejina, Babban Jami’in Kula da Sana’o’i da Sadarwa na Rukunin Dangote ya ce har yanzu kamfanin na NNPC bai fara dauke mai daga matatar man ba.

A cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu, Chiejina ya ce: “An jawo hankalinmu ga wani kanun labarai ‘NNPCL na daga man Dangote, ana sayar da shi kan Naira 897 kan kowace lita’, wanda aka buga a jaridar Business Day na Laraba, 4 ga Satumba, 2024.

“Muna so mu bayyana cewa, NNPC bai fara dauke matatun man fetur na Dangote ba, PMS, wanda aka fi sani da man fetur daga matatar man Dangote.

“Saboda haka batun kayyade farashin man fetur da aka daga matatar man bai taso ba domin har yanzu ba mu kammala kwantiragin mu da NNPC ba.

“Kasuwar PMS tana da kayyadaddun tsari wanda duk ‘yan kasuwar mai da masu ruwa da tsaki a fannin suka sani, don haka ba za mu iya tantancewa, gyara, ko tasiri farashin kayayyakin, wanda ke karkashin kulawar hukumomin gwamnati da abin ya shafa.”NNPCL ba

legit.news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp