Kungiyar kwadago ta kadsa NLC, ta yi tir da yajin aikin jami’o’i da ke ci gaba da tabarbarewa tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) yayin da ta bayyana shirin fara zanga-zangar kwanaki 2 a fadin kasar a ranar Talata 26 ga watan Yuli.
Zanga-zangar da aka shirya na da nufin tursasa Gwamnatin Tarayya ta kammala tattaunawa da kungiyoyin jami’o’in da ke yajin aiki da kuma tabbatar da cewa jami’o’in gwamnati sun koma gudanar da harkokinsu na yau da kullum da dai sauransu.
Wannan bayanin na kunshe ne a wata takardar da kungiyar NLC ta fitar ga daukacin shugabannin kungiyar na jihohi, mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar na kasa Ayuba Wabba da babban sakataren kungiyar, Comrade Emmanuel Ugboaja.