fidelitybank

NLC za ta gana da gwamnati a kan cire tallafin man fetur

Date:

Ana sa ran wakilan gwamnatin tarayya za su gana da shugabannin kungiyar kwadago ta kasa ta NLC a yau Laraba da karfe biyu na rana a kan shirin gwamnati na janye tallafin mai.

Shugaban kungiyar ta NLC, Joe Ajaero, shi ne ya bayyana haka a wata hira da tashar talabijin ta Channels ta yi da shi a yau Laraba.

Mista Ajaero ya ce tun da farko kamata ya yi a ce Shugaba Tinubu ya nemi sanin illa ko abin da zai iya biyo bayan cire tallafin ga talakawa Æ´an Najeriya kafin ya furta magana a kai.

Ya ce matsayin NLC a bayyane yake cewa idan har shugaban yana da kyakkyawar niyya da nufi a game da lamarin to kamata ya yi a ce an samar da wata madogara da Æ´an kasar za su karkata ga ita idan aka cire tallafin.

Shugaban na NLC ya bayyana wasu daga cikin abubuwan da ya ce kamata ya yi gwamnati ta yi kafin ta ambaci batun cire tallafin, abubuwan sun hada da gyara matatun kasar hudu samar da kyakkyawan tsarin sufuri ga ma’aikata da sauran tanade-tanade.

Furucin da Bola Tinubu ya yi a jawabinsa na farko bayan rantsuwar kama aiki ranar Litinin cewa babu sauran tallafin mai, ana ganin shi ne ya janyo jama’a suka shiga tururuwar sayen mai yayin da masu gidajen mai suka kara kudi,lamarin da ya haddasa dogayen layukan sayen mai a kasar.

A jawabin Shugaba Tinubun ya nuna cewa kasafin kudin da ya gada babu tallafin man, kuma kamar yadda gwamnatin da ya gada ta tsara daga watan Yuni babu sauran maganar tallafi.

tribune newspaper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp