Kungiyar Kwadago ta ƙasa (NLC), ta yanke shawarar mayar da gangamin ranar ma’aikata na 2022, zuwa ranar 2 ga watan Mayu idan majalisar koli ta harkokin addinin musulunci ta ƙasa ta sanar da ranar Sallah Eid-El-Fitr wadda aka fi sani da Ramadana a ranar 1 ga Mayu.
NLC ta ce, ta yanke shawarar ne, saboda yadda bikin Sallah ya kebanta da shi, domin kaucewa tarzomar bukukuwan.
Matsayin Majalisar na kunshe ne a wata takardar da aka aikewa dukkan shugabannin Majalisun dokokin kasar nan.
Da’awar ta samu sa hannun babban sakataren ta, Comrade Emmanuel Ugboaja.
Ya kara da cewa “A taron Kwamitin Ayyuka na Tsakiya (CWC) na Majalisar da aka gudanar a ranar 27 ga Afrilu, 2022, mambobin CWC sun yi nazari tare da tattaunawa kan yiwuwar fadowar Eid-El-Fitr Sallah a ranar 1 ga Mayu, 2022.