Kungiyar Kwadago ta bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin zuwa karshen watan Mayu da ta kammala aikin aiwatar da sabon mafi karancin albashin ma’aikata na kasar nan.
Shugaban kungiyar kwadago ta kasa na NLC, Joe Ajaero ne ya bukaci hakan a ranar Laraba a Abuja a bikin ranar ma’aikata ta duniya na shekarar 2024.
Shugaban kungiyar ya yi gargadin cewa, idan har ba a kammala tattaunawar ba a karshen watan Mayu, to ba za a samu zaman lafiya a masana’antu a Najeriya ba.
Ajaero ya ce, har yanzu ana ci gaba da kayyade sabon mafi karancin albashin ma’aikata.
Ya kuma ce, kungiyar na gabatar da bukatarta ga gwamnatin tarayya na albashin Naira 615,000 mafi karanci.
ga ma’aikata gwamnati a gaban abokan huldar mu yayin da muke jiran tayin su.
Ya ce kungiyar ta kuma bukaci duk wani ma’aikaci da ke aiki a wata ma’aikata, da a biya su sabon mafi karancin albashi.