Hukumomi a Jamhuriyar Nijar sun sanar da shirin ɗaukar sabbin dakarun soja 5,000 a rundunar sojan ƙasar a yaunƙurin gwamnati na yaƙar ‘yan bindigar da ke addabar yankuna daban-daban na ƙasar.
Akasari gwamnatin Nijar na ɗaukar mutum 2,000 ne duk shekara a aikin soja.
Hukumomi sun nemi matasa ‘yan shekara 18 zuwa 25 da su gabato da kansu don shiga aikin tsaron na soja da zummar kare ƙasarsu.
Matakin na zuwa ne yayin da Boko Haram ke ƙara tsaurara hare-hare a garuruwan da ke kudancin ƙasar masu iyaka da Najeriya da kuma ƙungiyoyin masu iƙirarin jihadi ƙawayen IS da al-Ƙa’ida a yammaci da ke da iyaka da Mali da Burkina Faso.
A cewar wata sanarwar gwamnati, za a fara ɗaukar sabbin dakarun daga watan Mayu mai zuwa.
Ficewar sojojin Faransa da ke yaƙi da masu iƙirarin jihadi a Mali ta jawo giɓi na tsaro bayan shafe shekara kusan 10. In ji BBC.