Gwamnatin Nijar ta sanar da rage kashe kudaden da take shirin kashewa a shekarar 2023, inda ta rage kasafin kudinta da kashi 40 cikin dari.
Wannan shawarar ta zo ne bayan takunkumin da kasashen duniya suka kakaba wa kasar bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a watan Yuli.
Gwamnatin mulkin sojan ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da aka watsa ta gidan talbijin a ranar Asabar din da ta gabata.
Sojojin sun sanar da rage kasafin kudin daga dala biliyan 5.3 (£4.3bn) zuwa dala biliyan 3.2, duk da cewa ba a samu cikakkun bayanai na rage kuɗaɗen ba.
Akalla kashi 40 cikin 100 na tallafin kasafin kudin kasar Afirka ta Yamma ana sa ran zai fito ne daga abokan huldar waje.
Juyin mulkin da ya hamɓarar da shugaba Mohamed Bazoum ya janyo hukumomi kamar kungiyar ECOWAS da Tarayyar Turai da Amurka sun sanya takunkumi da datse kadarori, da rufe kan iyakokin ƙasar da kuma dakatar da kayan agaji.
Wadannan matakan sun haifar da tashin gwauron zabin abinci da karancin kayan masarufi, da suka hada da magungunan ceton rai.
Gwamnatocin sojoji da ke makwabtaka da Mali da Burkina Faso dai sun goyi bayan juyin mulkin Nijar.