Gwamnatin sojin Nijar ta soke fasfunan tafiye-tafiye na jami’an hamɓararriyar gwamnati sama da 990 da suka haɗa da ƴan ƙasar da kuma ƴan ƙasashen ƙetare da suke da alaƙa da gwamnatin.
Bayanin na ƙunshe ne a cikin wani saƙo da ma’aikatar harkokin wajen Nijar ɗin ta wallafa a shafukan sada zumunta.
Waɗanda lamarin ya shafa sun haɗa da manyan jami’an hukumomi da cibiyoyi da tsoffin daraktoci da masu bayar da shawara ga hamɓarren shugaban ƙasar, Mohammed Bazoum.
Daga cikin waɗanda lamarin ya shafa akwai ƴan Amurka da Birtaniya da Faransa da kuma Libya da Turkiyya da wasu daga cikin ƙasashen Yammacin Afirka 50.
Sojoji sun hamɓarrar da gwamnatin shugaba Mohammad Bazoum a ranar 26 ga watan Yulin, kuma ana ci gaba da yi masa ɗaurin talala a gidansa.
A ƙarshen watan Agustan da ya gabata, sojojin sun soke fasfunan jami’an gwamnatin da dama waɗanda ke a ƙasashen waje da suka haɗa da firaminista da ministan harkokin wajen da kuma ambasadan Nijar a Faransa. In ji BBC.


