Shugaban mulkin sojin Nijar Abdourahamane Tchiani ya haramtawa wasu ƴan ƙasar mutum tara bayyana kan su a matsayin ƴan Nijar, bayan da ya ƙwace shaidar zama ƴan ƙasar na su.
Wadanda lamarin ya shafa sun haɗa da tsohon ministan ma’aikatar yawon buɗe ido,Rhissa Ag Boula, da Ighazer Hamidine Abdou.
Gwamnatin dai ta zarge su da aikata ta’addanci da cin amanar ƙasa da karya dokokin ƙasa.
A watan Agusta ne Janar Tchiani ya sanya wa dokar korar duk wani ɗan Nijar da aka samu da hannu wajen cin amanar ƙasar.
Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Human Rights Watch ta ce dokar wani salo ne na tauye haƙƙin ƴan ƙasar.
Hakan na nufin yanzu dai mutanen da aka kora din ba su da wata ƙasa da za su bayyana a matsayin ƙasarsu.