fidelitybank

Nijar ta kashe Lakurawa bayan sun tsere daga Najeriya

Date:

Rundunar sojin Jamhuriyar Nijar ta bayyana cewa jami’anta sun kashe ƴan Lakurawa – waɗanda suka shiga ƙasar ta kudu maso yammaci, kamar yadda kafar Tamtan.info mai zaman kanta ta ruwaito a ranar 25 ga Nuwamba.

Rundunar ta ce sun kashe mayaƙan ƙungiyar a ranar 21 ga Nuwamba a Muntseka, na yankin Illela da ke kudu maso yammacin jihar Tahoua da ke kan iyakar ƙasa da Najeriya.

Rahoton ya ƙara da cewa, “ƴan ta’adda ne da ake kira Lakurawa ko Lukurawa da suka ɓulla a jihohin arewa maso yammacin Najeriya musamman, Kebbi da Sokoto da suke da iyaka da jihohin Jamhuriyar Nijar wato Dosso da Tahoua, inda suka kashe mutum 15.

“Wataƙila sun gudu ne daga Najeriya suka shiga Nijar domin tserewa daga yaƙarsu da sojojin Najeriya ke yi,” in ji rahoton.

Lakurawa sun ɗauki alhakin wasu hare-hare a jihohin Kebbi da Sokoto, kuma suna ikirarin alaƙa da ƙungiyar Ansaru wadda ke samun goyon bayan ƙungiyar al-Qaeda.

today nigeria news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

A dawo da tallafin aikin Hajji ga maniyyatan Najeriya – Ndume

Jagoran ƴan kwamitin majalisar dattijawa kan harkokin ƙasashen waje...

A na fargabar mutuwar dukkanin fasinjojin jirgin Indiya da ya yi hatsari

Kamfanin dillancin labaru na AP ya rawaito cewa, shugaban...

An kwashe wasu daga cikin Gawarwakin da Jirgi ya fada cikin gidaje a Indiya

Ƙungiyar likitoci ta ƙasar Indiya (FAIMA), ta ce an...

Tinubu ya mayar da martani kan mayar da Najeriya tsarin jam’iyya daya

Shugaban kasa, Bola Tinubu ya mayar da martani game...

Zan cigaba da sa yawan jini ga maƙiya Tinubu – Wike

Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya sha alwashin...

Tinubu zai magantu a kan ranar Dimokradiyya

Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, zai yi jawabi ga...

A shirye nake na mutu don nasarar APC a 2027 – Orji Kalu

Sanatan Abia ta Arewa, Orji Uzor Kalu, ya bayyana...

Bayan hutun Sallah Tinubu zai koma Abuja

Shugaban ƙasa, Bola Tinubu na kan hanyarsa ta komawa...

Mutane 570 aka kashe a Najeriya cikin watan Afrilu – Rahoto

Hukumar kare haƙƙin ɗan'adam a Najeriya ta ce, adadin...

PDP ba za ta mutu ba duk da rikicin cikin gida – Wike

Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya ce...

Sojoji sun kashe riƙaƙen ɗan bindiga Guddel a Kaduna

Sojoji sun yi nasarar kawar da fitaccen shugaban ‘yan...

Fadar shugaban ƙasa ta yi kakkausar gargaɗi a kan Ndume

Fadar shugaban kasa ta yi kakkausar gargadi ga dan...
X whatsapp