Gwamnatin soji a Nijar ta zargi Faransa da a bin da ta kira jan ƙafa wajen janye sojojin ta daga ƙasar.
A wata sanarwa da sojin da sukai juyin mulki suka fitar, sun ce har yanzu babu alama ko shirin janye dakarun da aka cimma a farkon watan nan tsakanin su da kwamandan sojojin Faransa a yankin Sahel.
Sanarwar ta ƙara da cewa tsohuwar uwar gijiyarta na nuna turjiya a fakaice kan batun.
Dangantaka ta yi tsami tsakanin ƙasashn biyu, sun bayan sojoji sun hamɓarar da gwamnatin shugaba Muhammad Bazoum tare da tsare shi, tun a watan Yuli da ya wuce.
An dai ta yin zanga-zanga musamman a birnin Yamai, ciki har da sansanin sojin Faransar da ‘yan ƙasar suke kiraye-kiraye kan sojojin Faransar su fice daga Nijar.


