fidelitybank

Nijar ta bukaci Togo ta roki ECOWAS a sasanta

Date:

Gwamnatin sojan Nijar ta nemi shugaban ƙasar Togo, Faure Gnassingbe ya shiga tsakani a tattaunawa da ƙasashen duniya musamman ma ƙungiyar raya tattalin arzikin Afrika ta Yamma (Ecowas) wadda ta kakaɓa wa Nijar takunkumi tun bayan juyin mulki.

Ministan tsaron Nijar, Janar Salifou Mody ne ya bayyana haka lokacin da yake ganawa da Shugaba Gnassingbe a Lome babban birnin kasar ranar Litinin. Ya kuma nemi Togo ta tsayawa Nijar a yarjejeniyar janye sojojin Faransa daga kasar ta yankin Sahel.

“Yana da muhimmanci a koyaushe mu tunatar da abokan kawancenmu cewa, kofar Nijar a buɗe take, ko da an yi kulle-kullen da ba za mu iya magana da abokan hulɗarmu ba,” Mody ya shaida wa manema labarai bayan kammala taron.

Kungiyar Ecowas ta sanya wa Nijar takunkumin tattalin arziƙi da kuma rufe harkokin kasuwanci na kan iyaka da Nijar a yunƙurin matsa wa shugabannin kasar lamba har sai sun mayar da mulkin dimokradiyya.

Togo, duk da kasancewarta mamba a kungiyar Ecowas, ta dauki wasu matakai na hadin gwiwa da shugabannin sojojin Nijar tare da bayyana aniyar hawa teburin tattaunawa.

Tuni dai Faransa ta fara janye dakarunta 1,500 daga Jamhuriyar Nijar, bayan da gwamnatin mulkin sojan ƙasar ta buƙaci su fice jim kadan da hamɓarar da Shugaba Mohamed Bazoum a ranar 28 ga watan Yuli.

Ministan harkokin wajen Togo, Robert Dussey ya ce kasarsu a shirye take ta taimaka wajen tattaunawa.

“Togo na adawa da duk wani matakin juyin mulki” in ji shi. “Amma a yanayi na musamman na ƙasarku, Togo ta fahimta, kuma tana son taimaka muku.” in ji ministan

Shugaban Najeriyar, Bola Tinubu, wanda kuma shi ne jagoran Ecowas, ya bayyana taka-tsantsan wajen mu’amala da Nijar saboda damuwar da ake da ita dangane da hamɓaras da Shugaba Bazoum daga kan mulki.

Gwamnatin mulkin soja a Nijar ta ce za ta miƙa mulki bayan shekara uku hannun farar hula, yayin da ƙungiyar Ecowas ta buƙaci a gaggauta mayar da aiki da tsarin mulki.

Duk da haka, ana ci gaba da ƙoƙarin diflomasiyya don ganin a shawo kan lamarin.

daily post

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp