Gwamnatin mulkin sojin Jamhuriyar Nijar ta rattaba hannu kan wata yarjejeniyar ƙarfafa haɗin gwiwa tsakaninta da Iran wajen yaƙi da ta’addanci.
Haka kuma yarjejeniyar za ta ƙunshi yaƙi da miyagun laifuka da kuma kula da shige da fice ba bisa ƙa’ida ba.
A jiya ne ƙasashen biyu suka cimma wannan matsaya yayin wata ganawa tsakanin ministan harkokin cikin gida na Nijar da tawagar Iran a ƙarƙashin jagorancin Birgediya Janarar Ahmad Reza Radan a birnin Yamai.