Ƙasashen Nijar da Mali da Burkina Faso sun ƙaddamar da sabuwar ƙungiyar ƙawancen sojin ƙasashen yankin Sahel.
Ƙasashen sun amince da kafa ƙungiyar ‘Alliance of States of the Sahel’ (AES) wato ‘Ƙawancen ƙasashen yankin Sahel’, bayan wani taro da suka gudanar a birnin Bamako na ƙasar Mali. In ji BBC.
Taron – wanda ya samu halartar shugaban gwamnatin mulkin sojin Mali Kanal Assimi Goita, da ministocin ƙasashen wajen Mali da Burkina Faso da mai magana da yawun gwamnatin mulkin sojin Nijar – ya amince da kafa ƙungiyar don kare ƙasashen yankin Sahel.
Manufar kafa ƙungiyar ita ce samar da tsaron ‘haɗin gwiwwa’ tsakanin ƙasashen uku, ta hanyar yin aiki tare domin yaƙar ‘ta’addanci’ da ‘yan tawaye a cikin ƙasashen uku.
Haka kuma ƙungiyar ta amince da kai wa juna agaji idan ta samu farmaki daga waje.
“Duk wani hari da aka kai wa ɗaya daga cikin ƙasashen ƙungiyar , AES za ta ɗake shi ne tamkar hari a kan duka mambobinta, don haka za ta ɗauki matakin ramuwar gayya, a ƙungiyance ko daban-daban, ciki har da amfani da ƙarfin soji domin tabbatar da zaman lafiya a ƙasashe mambobin ƙungiyar,” kamar yadda yarjejeniyar ta nuna.
Ana kallon kafa wannan ƙawance tamkar martanin ƙasashen uku ne, kan barazanar da Ecowas ke yi na amfani da ƙarfin soji, don mayar da Nijar kan tafarkin dimokraɗiyya bayan da sojojin ƙasar suka kifar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Mohamed bazoum cikin watan Yuli.


