Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika, ya musanta zargin cewa aikin samar da kamfanin jirgin saman Najeriya na ‘Nigeria Air’ da gwamnatin tsohon shugaban ƙasar Muhammadu Buhari ta ƙaddamar a zamaninta na bogi ne.
Sirika, wanda ya rike mukamin minista sau biyu, ya bayyana hakan ne ga gidan talabijin na Channels a ranar Talata inda ya ce an bi dukkan ƙa’idoji.
Ya ƙara da cewa aikin samar da jirgin saman haɗin gwiwa ne tsakanin gwamnati da masu zaman kansu, ƙarƙashin kulawar hukumar tafiyar da hadin gwiwa tsakanin gwamnati da masu zaman kansu.
Tsohon ministan ya musanta batun cewa ya kashe naira biliyan 100 wajen aikin inda ya ce jimillar kuɗin da aka yi kasafi domin aikin samar da kamfanin sufurin shi ne naira biliyan 5 inda aka saki naira biliyan 3 kuma ya bar fiye da biliyan ɗaya lokacin da ya sauka daga muƙaminsa.
An kaddamar da Nigeria Air a ƙarshen mulkin Buhari, duk da cewa wasu sun ce aikin na bogi ne da kuma zamba.
Tun bayan ƙarewar wa’adinsa na minista a 2023, Sirika ya riƙa fuskantar shari’a kan zargin almundahana da amfani da mukaminsa ba bisa ka’ida ba.
Hukumar EFCC ta zarge shi da bai wa kamfanonin ‘yan’uwansa, ciki har da ‘yarsa kwangiloli da suka kai na biliyoyin naira.