Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican, Donald Trump, ya sha alwashin lashe zaben Amurka a watan Nuwamba.
Trump ya yi magana ne a lokacin da yake daukar mataki a babban taron jam’iyyar Republican a ranar Juma’a bayan ya amince da nadinsa na tsayawa takarar shugaban kasa.
Da yake jawabi ga taron jama’a a Milwaukee da ke Wisconsin, Trump ya ce: “Na tsaya a gabanku da yammacin yau da sakon kwarin gwiwa, da karfi, da kuma bege.
“Watanni hudu daga yanzu, za mu sami nasara mai ban mamaki, kuma za mu fara shekaru hudu mafi girma a tarihin kasarmu.”
“Tare, za mu kaddamar da wani sabon zamani na aminci, wadata da ‘yanci ga ‘yan ƙasa na kowace kabila, addini, launi da akida.”
Ku tuna cewa tsohon shugaban na Amurka ya tsallake rijiya da baya a wani yunkurin kashe shi a lokacin yakin neman zabensa a garin Butler na jihar Pennsylvania.