Rabiu Kwankwaso, dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar New Nigeria People’s Party, ya ce, yana da tabbacin samun nasara a kan Bola Tinubu da Atiku Abubakar a 2023.
Kwankwaso, wanda kuma shi ne jagoran tafiyar Kwankwasiyya, a wata hira da jaridar Punch, ya ce, shi ne ke da martabar rushe APC da PDP.
Ya kuma bayyana cewa, sanya hannu kan dokar zabe zai yi wahala kowa ya kayar da shi ta hanyar magudi.
Kwankwaso ya ce: “Kungiyar Kwankwasiyya ta shahara sosai, kuma za mu yi nasara a yankin Arewa maso Gabas. Na yi farin ciki da aka sanya hannu kan dokar zabe ta zama doka, kuma hakan zai yi wahala kowa ya yi mana magudi kamar yadda suka saba yi a baya.
“Da zarar an yi zabe na gaskiya da adalci, zai yi wahala wani ya kayar da mu. Don haka ina da tabbacin samun nasara a kan ‘yan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress, Bola Tinubu, da Atiku Abubakar na babbar jam’iyyar adawa ta Peoples Democratic Party, a zaben 2023″. In ji Kwankwaso.
Tsohon Gwamnan na Kano ya kuma bayyana cewa, ba zai yi janyewa kowa ba, domin a kayar da jam’iyyar APC mai mulki.