Tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya ce, shi ne uban matasan Najeriya da ke cikin takaici, saboda tabarbarewar tattalin arzikin kasar.
Kamar yadda wani faifan bidiyo da ya ke zagayawa a shafukan sada zumunta ya nuna tsohon shugaban kasar ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da wasu matasa karkashin jagorancin Charles Chukwuemeka Oputa wanda aka fi sani da Charly Boy.
Charly Boy wanda ya yi ikirarin cewa shi ne shugaban matasan Najeriya masu takaici ya roki Obasanjo da ya ba da shawarar hanyoyin da za a bi don magance wahalhalun da ake fuskanta a kan matasan.
A cewar mawakin, matasan da suka hada da kansa sun riga sun shiga damuwa, saboda rashin aikin yi da ke karuwa.
Da yake magana, Obasanjo ya zargi shugabannin Najeriya da tabarbarewar tattalin arziki, yana mai cewa ba laifin Allah ba ne, amma masu mulki ne.
A cewarsa, hanya daya tilo da za a tabbatar da sauyi ita ce kafa gwamnati ta gari ta hanyar shugabanni nagari.
Ya bayyana kwarin gwiwar cewa, matasan suna iya kawo canjin da ake bukata, yana mai cewa “babu wanda zai yi sai matasa”.
“Kai ne shugaban matasan Najeriya masu takaici kuma ni ne mahaifinsu.
“Cewa mu talakawa da takaici ba laifin Allah bane illa zabin shugabannin mu ne idan kuma za ku canza hakan, ku canza al’amura, ku canza shugabanci. Mai tsafta da sauki,” Obasanjo ya kara da cewa.


