fidelitybank

Ni matasa suka fi yayi a kan Atiku – Dan takarar shugaban kasa a PDP

Date:

Ɗan jarida kuma mawallafin mujallar Ovation Magazine, Dele Momodu, ya ce shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa da matasa suka fi yayinsa a Najeriya.

Momodu ya bayyana hakan ne ranar Alhamis ta kafar talabijin ta Channels, jim kaɗan bayan ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar PDP mai adawa.

Da a ka tambaye shi ko zai iya ja da gogaggu kuma manyan ‘yan siyasa kamar su, Atiku Abubakar, Mista Momodu ya ba da amsa da cewa, shi a ka fi yayi a Najeriya.

“Ba na so na yi alfahari. Babu wanda ake yayi kamata, ni ne wanda aka fi yayi a Najeriya. Ba wai ina magana a cikin PDP ba,” in ji shi.

Tun farko Dele Momodu ya kai wa shugaban PDP na ƙasa, Ayorchia Ayu, ziyara a sakatariyar jam’iyyar da ke Abuja, inda ya miƙa masa wasiƙar nuna sha’awar tsayawa takarar a hukumance.

Ɗan jaridar ya yi takarar shugaban ƙasa a babban zaɓen 2011 ƙarƙashin jam’iyyar National Conscience Party (NCP). A cewar BBC.

A na sa ran gudanar da babban zaɓen a Najeriya cikin watan Fabarairu da Maris na shekarar 2023, inda PDP za ta nemi ƙwace mulki daga hannun APC ta Shugaba Buhari.

naija news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp