Dan wasan tseren gudun Jamaica, Usain Bolt, ya ce, ya ji takaicin Cristiano Ronaldo da ya bar Manchester United.
Kyaftin din na Portugal ya bar Old Trafford ne, bisa amincewar juna a watan da ya gabata bayan wata hira da aka yi da shi wanda ya caccaki kungiyar da kocin Erik ten Hag da dangin Glazer.
Bolt wanda sau takwas ya lashe lambar zinare a gasar Olympic, kuma mai goyon bayan United, ya ce, ya ji takaicin ficewar tauraron, amma ya jaddada cewa ya fahimci dalilansa.
“Abin bakin ciki ne ganin ya tafi ya taka mana muhimmiyar rawa a kakar wasan da ta gabata, ya ajiye mu a gasar Premier a kakar wasan da ta wuce, saboda wasanni da dama shi ne ya ci.
“Don haka ganin ya tafi abin bakin ciki ne, amma na fahimci ta hanyar sauraron hirarsa akwai abubuwa da yawa da ke faruwa wadanda yawancin mu ba mu sani ba.
“Ina yi masa fatan alheri a tafiyarsa, saboda ni babban masoyin Cristiano Ronaldo ne. Don haka abin bakin ciki ne ganin ya tafi.”