Dakataccen gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara ya ce, babu wata sadaukarwa da ba zai yi ba, matuƙar za ta zama sanadiyar samar da zaman lafiya da ci gaba jihar.
Fubara, ya bayyana haka ne a Fatakwal a ranar Asabar lokacin da yake yi wa magoya bayansa jawabi, inda ya nanata musu cewa lallai sun sasanta da Ministan Abuja Nyesom Wike.
Ya ce ya san akwai wasu masoyansa da ba za su ji daÉ—in sasancin ba, sai ya ce su yi haĆ™uri domin, “wasu lokutan dole a É—auki matakan da ba za a ji daÉ—insu ba domin gyara,” in ji shi kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
“Kowa ya san mun iya bakin Ć™oĆ™arinmu, mun duk abin da ya kamata. Amma yanzu maganar gaskiya babu abin da muke buĆ™ata sai zaman lafiya.”
“Babu wanda zai shafe irin gudunmuwar da Ministan Abuja Nyesom Wike ya ba ni. Lallai mun samu saÉ“ani a kan wasu abubuwa, amma babu wanda zai ce bai irin rawar da mutumin nan ya taka ba, da irin Ć™alubalen da ya fuskanta. Don haka duk wanda yake Ć™aunata da gaskiya ya ajiye karinsa, yanzu lokaci ne na neman zaman lafiya.”