Fitaccen ɗan ƙwallon duniya Cristiano Ronaldo ya ce, shi da babban abokin hamayyarsa a fagen ƙwallon ƙafa, Lionel Messi “sun sauya tarihin ƙwallon ƙafar duniya”, to sai dai ya ce yanzu adawa tsakaninsu ta ‘wuce’.
‘Yan wasan biyu da ake yi wa laƙabi da GOAT ‘yan wasan da suka fi shahara a tarihi, sun sha fuskantar juna a lokacin da suke buga gasar La Liga a ƙungiyoyin Real Madrid da Barcelona.
“Dukkanmu ana girmama mu a duniya, wannan shi ne babban abu mafi muhimmanci”, in ji Ronaldo.
Ronaldo – wanda ya lashe kyautar Ballon d’Or har sau biyar – a bana baya cikin mutanenda ke takarar kyautar karon farko tun 2003, yayin da Messi zai iya lashe kyautar karo takwas a tarihi


