Ndubuisi Wilson Uwadiegwu da ake zargi da kashe matarsa Ogochukwu Uwadiegwu ya musanta laifin da ake zarginsa da ya yi.
Uwadiegwu ya shaidawa BBC cewa babu shaka sun samu sabanni tsakaninsa da matarsa har ta kai ga sun yi rikici, amma kam ba kan burodi ba ne kuma ba shi da hannu a mutuwarta.
A makon da ya gabata ne labarinsa ya rinka jan hankali a shafukan sada zumunta kan miji ya kashe matarsa saboda burodi.
‘Yan uwan matar da BBC ta tuntuba sun shaida cewa lamarin ya faru ne a Disamba 2022, a jihar Enugu da ke kundacin Najeriya.
A cewar Chukwuebuka sun soma rikicin ne bayan matarsa ta bukaci ya siya mata burodi amma sai ya ce mata ba shi da kudi.
Sai matar tayi amfani da kudinta ta saye burodi, sai kawai mijin ya cinye burodin.
Daga nan ne aka soma rigima har ta kai ga ta fadi madubi ya yanketa. Sannan ya doke diyarsa yar shekara 14 ne saboda ta zageshi a lokacin da suke rigima da matarsa.
Mutumin dai ya ce ajali ne kawai ya zo amma ba wai shi ne ya yi sanadin mutuwar matarsa ba.