Shugaban jamâiyyar PDP na kasa, Sanata Iyorchia Ayu ya musanta karbar Naira biliyan 1 daga hannun kowa kamar yadda gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ya yi ikirari, yana mai gargadin wadanda suka fusata da su bar iyalansa daga cikin rigimar.
Ayu ya karyata ikirarin Wike yayin da yake amsa tambayoyi game da zargin da ake masa sannan ya kuma yi alkawarin cewa za a gabatar da bayanin asusun jamâiyyar ga mambobin jamâiyyar nan ba da jimawa ba.
Shugaban PDP na kasa ya ce a matsayinsa na uban jamâiyyar ya yanke shawarar yin shiru domin zaman lafiya ya yi mulki.
Ayu ya kuma yi kira ga daukacin âyaâyan jamâiyyar da su bar iyalansa da cewa. “Na ga ya kamata in karfafa sulhu. Amma inda ya shafi mutuncina, wanda har âyan uwana ake kawo su cikin wasa.
âIna kira ga mutanen da suka fusata su daina yunkurin bata min hali ko shigar da iyalina cikin harkokin jamâiyya.
â Ban taba karbar biliyan 1 daga hannun kowa ba. Kuma miliyan 100 da daya daga cikin gwamnonin ya bayar, an yi amfani da shi bisa ga adalci wajen abin da aka bayarâ.