Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya ce, bai kai karar dan takarar shugabancin jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar da gwamnan Sokoto Aminu Waziri Tambuwal kotu ba.
Ya bayyana hakan ne yau Juma’a a wani wajen taro da manyan jam’iyyar a birnin Port Harcourt.
Ya kara da cewa bai bai wa kowa izinin kai ƙararsu kotu ba.
Tun da fari, wasu jaridu sun rawaito cewa, Wike da wani ƙusa a PDP mai suna Newgent Ekamon sun shigar da ƙara mai lamba FHC/ABJ/CS/782/2022 da ke kalubalantar janyewar Tambuwal daga zaɓen fitar da gwani da kuma goyon bayan Atiku.


