Marcus Rashford ya zama wani gwarzo da ya fito daga benci, kuma ya ci wa United kwallo guda a wasan da ta buga Wolves wanda hakan ya ba ta damar koma wa ta hudu a gasar Premier.
Koci Erik ten Hag ya ajiye Rashford a benci a farkon wasan, a matsayin wani hukunci na saba doka da dan wasan yayi.
Dan wasan ya sauya Alejandro Garnacho wanda ya samu damar cin kwallo amma ya gaza ci mai tsaron raga Jose Sa ya hana ta ci, ya ci kwallo ne minti 14 da shigarsa cikin wasan.
Dan wasan ya rubuta a shafinsa na Intanet cewa, ya yayi barci har ya makara lokacin da aka fara lamuran wasa, kuma ya yarda da cewa hukuncin da aka yi masa babu son rai a ciki.
Ya zuwa yanzu Rashford ya ci kwallo 11 a duka wasanni da ya buga a wannan kakar.
Wannan ne karon farko da dan wasan ya ci kwallo uku a cikin wasanni uku a jere tun wanda ya yi a watan Disambar 2019.n