Shugaban wasanni Tayo Adeyemo ya bukaci hukumar kwallon kafa ta Najeriya, NFF, da ta rike kocin Super Eagles, Jose Peseiro.
Ya ce tsawaita kwantiragin Paseiro zai taimaka wa Super Eagles wajen tunkarar gasar AFCON na gaba.
Adeyemo ya bayyana haka ne a ranar Laraba a Legas yayin da yake zantawa da NAN.
Ya kuma bukaci hukumar ta NFF da ta mayar da hankali wajen fitar da ‘yan wasan gida da za su lashe gasar cin kofin Afrika na gaba, AFCON, da za a yi a Morocco.
“Morocco za ta karbi bakuncin gasar cin kofin nahiyar Afirka karo na 35 na Total Energies CAF ko kuma gasar cin kofin Afrika a shekarar 2025. Ya kamata NFF ta tsawaita kwantiragin kocin,” in ji shi.
Ya bukaci Super Eagles da NFF su mayar da hankali kan gasar AFCON na gaba da wasannin share fage idan har kungiyar ta zarce tarihin da ta samu a baya.
Adeyemo ya ce kungiyar na bukatar karin ‘yan wasa kwazo da kwarewa da jajircewa domin lashe kofin a yunkurinsu na gaba.
Ya ce: “Ya kamata su kara yin shiri kan horo da buga wasannin sada zumunta akai-akai tare da ‘yan wasan gida idan ‘yan wasan duniya ba su shirya ba.”
Adeyemo ya ce Super Eagles ta yi rawar gani wajen samun matsayi na biyu a gasar AFCON ta 2023 da Cote d’Ivoire ta karbi bakunci.
“Kafin gasar da yawa daga cikin ‘yan Najeriya ba su yi tsammanin kungiyar za ta kai wasan karshe ba ko ma ta tsallake zuwa matakin rukuni.
“Don kungiyar ta kai wasan karshe, hakan na nufin kociyan ya taka rawar gani, kuma ya kamata a ci gaba da rike shi,” in ji shi.