A ranar Talata ne hukumar kwallon kafa ta kasa (NFF), ta fitar da jadawalin wasannin gasar cin kofin tarayya na shekarar 2023.
Za a fara zagayen farko da na karshe na gasar a matakin jiha a ranar 18 ga Maris kuma za a kare ranar 19 ga Maris, 2023.
Ƙungiyoyi biyu ne za su wakilci kowace jiha a matakin ƙasa.
Ana sa ran Hukumar FA ta Jihohi za ta mika wakilan ta a ranar 20 ga Maris.
Hukumar ta NFF ce za ta tantance ranakun da za a fitar da jadawalin na kasa.
Za a fara rajistar kungiyoyin a matakin jiha a ranar 16 ga Janairu, yayin da mika fom din ‘yan wasa don samar da lasisin ya kasance tsakanin 31 ga Janairu zuwa 6 ga Fabrairu, 2023.