Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta ƙasa (NFF), Ibrahim Gusau, ya tsawaita wa’adin kwamitin rikon kwarya na (IMC) har zuwa karshen kakar wasannin 2022/23.
IMC ta maye gurbin tsohon Kamfanin Gudanarwa na League (LMC) a bara.
Gusau ne ya kaddamar da sabuwar kungiyar a watan Oktoba 2022.
Gusau ya bayyana cewa, ya tsawaita wa’adin IMC ne domin baiwa kungiyar ta Gbenga Elegbeleye damar mayar da hankali kan tsari da tafiyar da kakar NPFL da ke gudana.
An fara kakar 2022/23 makonni kadan da suka gabata.
Za a buga wasannin mako na uku a cibiyoyi daban-daban guda 10 a Najeriya a karshen mako.


