Hukumar kwallon kafa ta Najeriya NFF ta bayar da sanarwar naɗa Jose Peseiro a matsayin sabon kocin Super Eagles.
Hukumar ta ce, Jose Peseiro wanda ɗan asalin ƙasar Portugal ne shi zai jagoranci Super Eagles. In ji BBC.
NFF ta sanar da matakin ne cikin wata sanarwa daga kakakinta Ademola Olajire.
Sanarwar ta ce zai fara jagorantar tawagar Super Eagles a ziyarar da za ta kai Amurka a wasannin sada zumunci.
Tsohon dan wasan Super Eagles Finidi George da Salisu Yusuf za su zama mataimakan sabon kocin.
Tun a watan Disamba Hukumar ƙwallon Najeriya ta fara sanar da naɗa kocin amma daga baya ta naɗa Augustine Eguavoen a matsayin kocin rikon kwarya domin ya ja ragamar Super Eagles a gasar cin kofin Afirka.
A watan Disamban 2021 NFF ta ce kwamitin zartarwata ne ya amince da naɗa Peseiro kuma zai zama mai sa ido kafin a dawo ya ci gaba.
Amma daga baya hukumar ta ce ta fasa saboda kwazon Augustine Eguavoen