Hukumar kwallon kafa ta kasa NFF, ta sanar da nadin Finidi George a matsayin sabon mai horas da tawagar Super Eagles.
Tsohon dan wasan na kasa ya doke Emmanuel Amuneke.
Finidi George, wanda ya shafe watanni 20 a matsayin mataimaki ga José Santos Peseiro kafin dan kasar Portugal ya bar mukamin da radin kansa, bayan Najeriya ta yin a biyu a gasar cin kofin kasashen Afrika a Cote d’Ivoire 2023.
Finidi Goerge, ya karbi ragamar horar da ‘yan wasan na wucin gadi na tsawon shekaru biyu.
Finidi George zai jagoranci Super Eagles zuwa ga nasara a wasanni biyu na neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya na 2026 da Najeriya za ta yi da Afirka ta Kudu da Jamhuriyar Benin a Uyo da Abidjan, nan da makonni biyar masu zuwa.
Wasan ya zama tilas ne a yi nasara, inda Super Eagles ke matsayi na uku a rukunin C na gasar cin kofin Afirka, bayan Rwanda da Afirka ta Kudu.