fidelitybank

Neymar ba zai bugaBrazil wasanni biyu ba – Likita

Date:

Neymar ba zai buga wasanni biyu na gasar cin kofin duniya da Brazil za ta buga ba, bayan da ya samu rauni a kafarsa ta dama, in ji likitan tawagarsu.

An maye gurbin dan wasan mai shekaru 30 a minti na 80 na wasan da suka doke Serbia da ci 2-0 a ranar Alhamis, bayan da Nikola Milenkovic ya yi masa ya yi masa keta.

Shi ma Danilo ba zai buga wasanni biyu masu zuwa ba saboda rauni a idon sawunsa.

Brazil za ta kara da Switzerland a wasansu na biyu a rukunin G ranar Litinin 4:00, kafin kuma ta kara da Kamaru ranar Juma’a mai zuwa 8:00.

“Neymar da Danilo sun yi gwajin MRI a ranar Juma’a da yamma kuma mun sami rauni a idon sawun su biyu,” in ji likitan tawagar Brazil Rodrigo Lasmar.

Da yake magana bayan nasarar da suka yi da Serbia, babban kocin Brazil Tite, ya ce, suna da yakinin cewa Neymar zai ci gaba da taka leda a gasar cin kofin duniya.

Dan wasan na Paris St-Germain ya samu raunuka da dama da kafarsa ta dama a shekarun baya.

Bai buga gasar Copa America ta 2019 ba, bayan ya sha fama da rauni a idon sawunsa na dama kuma ya yi jinyar makonni da yawa a cikin 2021 da irin wannan rauni.

legit news.com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Peter Obi na nan a cikin jam’iyyar har yanzu – LP

Shugaban ƙungiyar Obidient Movement, Dr. Tanko Yunusa ya ce...

Yadda Mahara sun kashe mutum biyu, sun ƙona gidaje a Filato

Wasu da ake zargin mahara sun afka wa karamar...

An YI zanga-zanga a Isra’ila kan shirin Netanyahu na mamaye Gaza

Dubban mutane sun fito kan tituna a faɗin Isra'ila,...

Birtaniya za ta fara tisa ƙeyar bakin da suka aikata laifi zuwa kasarsu

Birtaniya ta fitar da sabon tsarin tisa keyar duk...

NDLEA ta kama Fasto kan zargin safarar miyagun ƙwayoyi

Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Najeriya,...

Gwamnoni sun mika sakon ta’azziya ga iyalan Audu Ogbeh

Shugaban ƙungiyar gwamnonin arewa kuma gwamnan jihar Gombe, Muhammadu...

Duk wahala sai dai mu mutu a Gaza – Fatma

Wata mai mai ƴaƴa tara ta ce, duk runtsi...

Gwamnan Kano ya kori mataimansa na musamman kan belin Danwawu

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da...

Tsohon Minista a mulkin Buhari ya mutu

Allah ya yi wa tsohon ministan noma da raya...

Kashi 70 na yankin Bukuyum ta Kudu na ƙarƙashin ƴan Bindiga – Ɗan majalisa

Rahotanni daga yakin ƙaramar hukummar Bukuyum na jihar Zamfara...

Goodluck ya fi dacewa ya zama dan takara a 2027 – Lamido

Tsohon Gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido ya ce Tsohon...

An gargadi al’umma su yi taka tsan-tsan da ambaliyar ruwan sama

Yayin da ake ci gaba da fuskantar saukar ruwan...
X whatsapp