Hukumomin leƙen asirin ƙasashen Netherlands da Jamus sun zargi Rasha da amfani da makamai masu guba a yaƙin da take yi da Ukraine.
Sun ce Rasha na amfani da hayaƙi mai sa hawaye da kuma sinadarai mai haɗari na guba, da ke sanya tari da numfashi mai wahala.
Hukumar leƙen asirin Netherlands ta ambato hukumomin Kyiv na cewa, Rasha ta kai hare-haren makamai masu guba fiye da dubu tara (9,000) bayan mamayar Ukraine sama da shekaru uku (3) da suka gabata.
Hukumar leƙen asirin Netherlands ta zargi Rasha da amfani da makamai masu guba domin tilasta wa sojojin Ukraine fita daga mafaka, don a fi samun sauƙin halaka su.
Gwamnatin Netherlands ta ce irin wannan amfani da makamai masu guba barazana ne ga tsaron Turai da ma duniya baki ɗaya, kuma ba za ta amince da hakan ba.
Sai dai Rashan ta musanta zarge-zargen.