fidelitybank

Netanyahu ya sha alwashin mayar da martani kan harin da ƴan Houthi suka kai

Date:

Firaiministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya sha alwashin mayar da mummunan martani kan harin makami mai linzami da ƴan tawayen Houthi suka kai kusa da wani filin jirgin sama a Isra’ila.

A cikin wani bidiyo da aka wallafa a shafukan sada zumunta, Netanyahu ya yi barazanar far wa ƙungiyar, inda ya ce: “Mun kai hari a baya, za mu kuma sake kai hari a gaba”.

Makamin mai linzami da ƴan Houthi waɗanda ke samun goyon bayan Iran suka harba daga Yemen, ya faɗa kusa da filin jirgin sama a Ben Gurion ranar Lahadi da safe, a cewar hukumomi.

Lamarin ya jikkata mutum huɗu, yayin da wasu biyu suka jikkata a kan hanyar su ta zuwa wani matsuguni, a cewar kafofin yaɗa labaran Isra’ila.

Mai magana da yawun sojojin Houthi, Yahya Saree ya bayyana a wata sanarwa da aka watsa a gidan talabijin cewa “yanzu filin jirgin saman Isra’ila ba shi da tsaron da za a iya yin tafiye-tafiye”.

Ministan tsaron Isra’ila, Israel Katz, ya faɗa a wata sanarwa cewa: “Duk wanda ya kawo mana hari, za mu mayar da martani har sau bakwai”.

the nation news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Farfesa Jibril Aminu ya rasu ya na da shekaru 86

Allah ya yi wa Farfesa Jibril Aminu mai shekara...

Alhajin Najeriya ya rasu a tsayuwar Arfa

Wani Alhaji daga Najeriya ya rasu a filin Arfa...

Alhazai miliyan 1.673,230 ne ke gudanar da akin Hajji – GASTAT

Hukumar tattara alƙaluma ta Saudiyya (GASTAT) ta ce, Alhazai...

Isra’ila ta gano gawar ƴan ƙasarta

Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta gano gawar ''yan...

Ma’aikatan wutar lantarki a Abuja sun fusata

Ma'aikatar kamfanin rarraba wutar lantarki na Abuja Electricity Distribution...

Ƴan Najeriya 147 da suka maƙale a Nijar sun dawo gida

Gwamnatin Najeriya ta tarɓi 'yan ƙasar 147 aka kwaso...

Alhazai Miliyan Ɗaya da Rabi ke tsayuwar Arfa

Dubun dubatar alhazai daga sassan duniya na hawan Arafa...

Sarkin Kano na 15 ya dakatar da yin hawan Sallah

Mai martaba Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado...

Maniyacin jihar Kano da yake kokarin zama Alhaji ya rasu a Saudiyya

Daya daga cikin alhazan jihar Kano, Shu’aibu Jibrin, an...

Tinubu ya bayar da tallafin Biliyan Biyu da Tirela 20 na Shinkafa ga al’ummar Mokwa

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya ce, shugaban ƙasar...

Gwamna Adeleke na Osun ya gana da Tinubu

Gwamnan jihar Osun Ademola Adeleke ya kai ziyara ga...

An samu gawar mutane 7 a ambaliyar Neja

Rahotonni na cewa masu aikin ceto sun zaƙulo gawar...
X whatsapp