Benjamin Netanyahu ya zama firaministan Isra’ila na farko da ya gurfana a kotu kan zargin aikata manyan laifuka yana kan mulki.
Netanyahu ya shaida wa kotu a Tel Aviv cewa zargin rashawa da ake yi masa ba shi da tushe.
Masu shigar da ƙara sun ce Netanyahu ya amshi kyautuka masu tsada, ya kuma ba kafafen yaɗa labarai toshiyar baki domin su riƙa yabon sa.
Firaministan Isra’ilar ya yi ƙorafin cewa kafafen yaɗa labarai sun tsane shi saboda shi ba mai sassaucin ra’ayi ba ne.
Ya kuma yi bayani sosai kan yadda yake kwashe tsawon lokaci yana aiki ba tare da ya samu “ko da minti biyar tare da matarsa ba”.