Darakta-Janar ta Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa, NEMA, Zubaida Umar, ta ce, hukumar ta fara shirin aikin kwashe jama’ar da ke fuskantar barazanar ambaliyar ruwan sama zuwa kan tudu.
A daidai lokacin da a ke ci gaba da fuskantar mamakon ruwan sama, NEMA ta ce ambaliyar ruwa ta shafi jihohi 28, inda mutum 175 suka mutu, sannan mutum 207,902 suka rasa muhallansu.
Hukumar ta ce ambaliyar ta shafi mutum 526,703 a ƙananan hukumomi 133, inda lamarin ya shafi gidaje 79,138 da kuma hekta 106,178 na gonaki.
Domin fuskantar wannan yanayin ne, gwamnonin jihohi da NEMA ta fara kwashe mutane daga wuraren da suke fuskantar barazanar ambaliyar domin rage ɓarnar.
Ta ƙara da cewa NEMA za ta buɗe cibiyoyinta domin sauƙaƙa ayyukan hukumar domin jiran kar ta kwana.
Wannan na zuwa ne bayan ziyarar Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnatin Najeriya, Femi Gbajabiamila a hukumar, inda ya je domin duba yadda ake gudanar da ayyukan hukumar bayan wani taron ƙara wa juna sani da ya yi da hukumomin da ke ƙarƙashin Fadar Shugaban Ƙasa.
Darakta-Janar ɗin ta kuma buƙaci ƙarin haɗin kai daga kwamitin majalisa da sauran masu ruwa da tsaki domin faɗaɗa ayyukan NEMA da shirye-shiryenta na fuskantar ayyukan agajin gaggawa.