Hukumar bayar da agajin gaggawa ta NEMA ta sake karbar wasu ‘yan Najeriya 137 da suka makale daga kasar Libya.
Hukumar NEMA ta tabbatar da hakan a wata sanarwa da ta fitar ranar Talata a Legas.
Hukumar ta ce mutanen da suka dawo sun isa filin jirgin saman Murtala Muhammad, Cargo Wing, Ikeja, a cikin jirgin Al Buraq Air Boeing 737-800 da karfe 5.15 na yammacin ranar Litinin.
NEMA ta ce wadanda aka dawo da su sun hada da maza 80, mata 52 da jarirai uku.
Mista Mustapha Ahmed, Darakta-Janar na NEMA, wanda ya karbi mutanen da suka dawo a hukumance a madadin gwamnatin tarayya, ya shawarce su da su yi koyi da abubuwan da suka faru kuma su kasance masu bin doka da oda.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya bayar da rahoton cewa, an kwashe kusan ‘yan Najeriya 3,000 daga kasar Libya tun daga watan Janairu.
Har ila yau, rahoton ya ce a ranar Lahadi, NEMA ta karbi ‘yan Najeriya 542 da suka makale daga Hadaddiyar Daular Larabawa, UAE.


