Hukumar shirya jarabawar ta kasa (NECO), ta ce za a fitar da sakamakon jarabawar kammala sakandare ta shekarar 2023 ranar Talata.
NECO ta kammala gudanar da jarabawar ne a farkon watan Agustan 2023, kuma mutane 1,205,888 ne suka zana jarrabawar.
‘Yan takara dubu dari shida da saba’in da hudu maza ne, yayin da 584,814 mata ne.
Hukumar jarrabawar dai ta shirya fitar da sakamakon ne cikin kwanaki 45, amma alkawarin bai samu ba.
Sai dai NECO ta tabbatar da cewa za a fitar da sakamakon da misalin karfe 11 na safiyar yau.