fidelitybank

NECO za ta saki sakamakon daliban Zamfara

Date:

Gwamnatin jihar Zamfara ta bayyana cewa an kammala biyan kudin jarabawar hukumar shirya jarabawa ta kasa wato NECO a shekarar 2022, inda ta ce za a fitar da sakamakon a karshen wata.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwar manema labarai da kwamishinan yada labarai na jihar, Hon. Ibrahim Magaji Dosara.

Kwamishinan ya shawarci iyaye da masu kula da ‘yan takarar da suka zana jarabawar NECO ta 2022 da su tuntubi makarantunsu domin samun sakamakonsu a karshen watan Satumban 2022.

Ya yi nuni da cewa, don haka ya kamata wadanda abin ya shafa su rika samun sakamakonsu ta yanar gizo domin samun gurbin karatu a manyan makarantun gaba da sakandire kafin a fitar da takardar zuwa makarantu daban-daban daga hukumar shirya jarabawar ta jihar Zamfara.

Dosara, ya kuma yi kira ga iyaye da masu kula da su da su kara hakuri saboda ana ci gaba da tattaunawa don fitar da sakamakon jarabawar NECO na 2021.

Sanarwar ta kara da cewa, “Gwamnatin jihar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen ganin an farfado da fannin ilimi a jihar ta hanyar sauye-sauye daban-daban.”

dailypost news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp