Hukumar shirya jarabawa ta kasa (NECO) ta kara wa’adin rajistar jarrabawar kammala sakandare (SSCE) na shekarar 2022.
PlatinumPost ta ba da rahoton cewa, lokacin rajistar yanzu zai zo ƙarshen tsakar daren Litinin 20 ga watan Yuni, 2022.
Hakan ya fito ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban yada labarai da hulda da jama’a na NECO, Mista Azeez Sani, wanda aka rabawa manema labarai a Abuja ranar Litinin.
Tun da farko an shirya rufe wa’adin rajistar ranar Litinin 30 ga Mayu, 2022.