fidelitybank

NECO ta fitar da sakamakon jarrabawar 2024

Date:

Hukumar shirya jarrabawar kammala sakandire ta NECO, ta fitar da sakamakon jarrabawar wannan shekara.

Hukumar ta ce sakamakon ya nuna kashi 60.55 na ɗaliban da suka rubuta jarrabawar sun samu kiredit biyar zuwa sama ciki har da daraussan Turanci da Lissafi.

Shugaban hukumar, Farfesa Dantani Ibrahim Wushishi ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai da ya gudanar a shalkwatar hukumar ta NECO da ke garin Minna na jihar Neja.

Farfesa Wushishi ya ce ɗalibai miliyan ɗaya da dubu ɗari uku da sittin da ɗari huɗu da ashirin da uku (1,376,423), ne suka rubuta jarrabawar ta bana.

”Daga cikin wannan adadin akwai maza 706,950 sai kuma mata 669,473”, in ji shi.

”Adadin ɗaliban da suka samu kiredit biyar zuwa sama ciki har da darussan Lissafi ta Turanci shi ne 828,284, waɗanda kuma suka samu kiredit biya zuwa sama ba tare da la’akari da darussan Turanci da Lissafi ba ya kai 1,147,597”, in ji shugaban na NECO.

Dangane da batun satar jarrabawa kuwa, Farfesa Wushishi ya ce a wannan shekarar an samu gagarumar raguwar matsalar idan aka kwatantwa da shekarar da ta gabata.

hausa

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp