fidelitybank

NECO ta fitar da sakamakon jarabawar 2022

Date:

Hukumar shirya jarrabawar NECO, ta fitar da sakamakon jarrabawar da aka yi ta watan Nuwamba da Disamba na 2022 ta daliban manyan makarantun sakandire.

Shugaban hukumar Farfesa Dantani Ibrahim Wushishi, shi ne ya sanar a Minna, babban birnin jihar Naija.

A bayanin da ya yi, ya ce a jumullar dalibai 59,124 suka yi jarrabawar, daga cikinsu 31,316 maza ne waÉ—anda yawansu shi ne kashi 52.96 cikin É—ari.

Yayin da mata suka kasance 27,808, kashi 47.03 cikin É—ari.

Farfesa Wushishi ya ƙara da cewa daga cikin yawan ɗaliban da suka rubuta jarrabawar harshen Ingilishi 58,012 guda 44,162, wato kashi 76.13 cikin ɗari sun samu kiredit zuwa sama.

Yayin da É—alibai 57,700, da suka yi jarrabawar lissafi guda 43,096, wato kashi 74.69 cikin É—ari suka ci kiredit zuwa sama.

Shugaban ya ƙara bayani da cewa yawan ɗaliban da suka ci kiredit biyar zuwa sama a duka jarrabawar da ta haɗa da Ingiishi da lissafi 33,914 wato kashi 57.36 cikin ɗari.

Hukumar ta NECO, wadda ta fitar da sakamakon jarrabawar bayan kwana 57, ta kuma ce an samu dalibai 11,419 da laiffukan da suka danganci satar jarrabawa, saɓanin 4,454 da aka kama 2021, wanda hakan ta ce ya nuna ƙaruwar matsalar sosai.

www.leadership ng.com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp