Hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire ta kasa, NECO, ta sake dage jarabawar shiga jami’o’in yara masu hazaka zuwa makarantar gwamnatin tarayya dake Suleja a shekarar 2023.
NECO ta dage jarabawar daga ranar Asabar 13 ga watan Mayu zuwa Asabar 10 ga watan Yuni 2023.
Shugaban sashen yada labarai da hulda da jama’a na NECO, Azeez Sani, ya ce an sake dage jarabawar ne domin baiwa ‘yan takara damar yin rijistar jarabawar sakamakon bukatar da wasu masu ruwa da tsaki suka yi na a tsawaita lokacin rajistar.
Sanarwar da Sani ya fitar ta ce: “Kwamitin Gwamnatin Tarayya da ke Suleja wuri ne na horar da yara masu hazaka da hazaka na Najeriya. Yana ba da dama mai yawa ga ƙwararrun ɗalibai masu hazaƙa don haɓaka ƙarfinsu don amfanin gina ƙasa da ci gaban fasaha.
“Daliban sun ci gajiyar tallafin karatu na Gwamnatin Tarayya kamar kudin makaranta, kudin jarrabawar waje, na kwana, ciyarwa, Unifos da kuma litattafan karatu.
“Don haka an umurci dukkan ‘yan takara, iyaye, masu kulawa da sauran masu ruwa da tsaki da su lura da sabuwar ranar da za a yi jarabawar.
“Za a ci gaba da rijistar ‘yan takara har zuwa sabon ranar da za a gudanar da jarrabawar.”