Hukumar Shirya Jarrabawa ta Kasa (NECO), ta ce, ta dage jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire ta kasa (NCEE) zuwa ranar Asabar 3 ga watan Yuni 2023.
A cikin wata sanarwa da shugaban sashen yada labarai da hulda da jama’a, Azeez Sani, ya fitar, hukumar ta dage jarabawar daga ranar Asabar, 29 ga Afrilu, 2023 zuwa 3 ga watan Yuni 2023.
A cewar sanarwar, canjin ranar da za a gudanar da jarabawar ya kasance ne domin baiwa jihohin da ke da karancin rajista damar yin rijistar wadanda za su yi jarrabawar.
Ta shawarci dukkan ‘yan takara, iyaye, masu kula da malaman makaranta da masu ruwa da tsaki da su lura da sabuwar ranar da za a gudanar da jarabawar.
“Za a ci gaba da yin rijistar ‘yan takara har zuwa ranar da za a gudanar da jarrabawar,” in ji Sani.