Hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi NDLEA ta ce, ta kama ƙwayar Tramadol kusan miliyan biyu tare da maganin tari na Codeine a filin jirgin sama na Muratala Muhammad da ke Legas.
Wata sanarwa da hukumar ta fitar a yau Laraba ta ce, an shigar da ƙwayoyin ne daga Pakistan da kuma Birtaniya.
Ta ƙara da cewa, an ƙwace kayan a ranar 10 ga watan Maris, inda aka samu ƙwaya samfurin Co-codamol 349,800 wadda gwamnati ta haramta.
Sai kuma a ranar 15 ga Maris, inda jami’an NDLEA tare da haɗin gwiwar na Kwastam suka kama ƙwayar Tramadol 1,584,000 a filin jirgin.
A gefe guda kuma, NDLEA ta kama wani ɗan shekara 50 da yunƙurin shigar da hodar ibilis mai nauyin 11.91kg zuwa Ghana ta kan iyakar Seme da ke Legas.
A cewar sanarwar, waɗanda suka yi safarar ƙwayoyin sun yi amfani da motar jigilar kaya ta cikin filin jirgi mai suna Skyway Aviation Handling Compnay (SAHCO).