Jami’an hukumar yaki da masu ta’ammali da miyagun kwayoyi ta NDLEA, sun kama wani fasinja a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe International Airport, da ke Abuja bayan da aka gano yana da alamun koken a cikinsa.
A wata sanarwa da kakakin hukumar ta NDLEA, Femi Babafemi, ya fitar yau Lahadi, ya ce mutumin, Paul Okwuy Mbadugha, mai shekar 54, wanda dan kasuwa ne da zai tafi Vietnam, ya shiga hannun hukumar ne a ranar Litinin 12 ga watan Agustan nan na 2024, yayin da yake shirin hawa jirgin Qatar Airways zuwa Vietnam, bayan yada zango a Doha.
Sanarwar ta kara da cewa: ”Bayan kwana hudu da aka sanya shi yana bahaya, Mbadugha ya kasayar da kullin koken 88 da nauyinsu ya kai kilgram 1.171.
Hukumar ta ce, a bahasin da mutumin ya bayar ya ce, shi dan kasuwa ne a Lagos kuma wani abokinsa ne a Isolo, ya ba shi kullin ya hadiye domin kaiwa Vietnam a kan kudi dala 2,000.
Haka kuma hukumar ta NDLEA ta ce, jami’ant sun kama wani babban kulli na na ganyen wiwi da nauyinsa ya kai kilogram 800, da aka boye a kwalayen taliyar yara, da nufin kaiwa kasar Kongo.
Hukumar ta ce, bayn da aka bi diddigin inda kayan ya fito an kama wani mutum mai suna Nnamani Sunday Sunny a kasuwar Alaba International market, a yankin karamar hukumar Ojo, a Lagos.